Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: "Saad Ma'an," shugaban cibiyar yaɗa labarai ta tsaro na Iraki a yau Asabar ya bayyana cewa: Hashdush-Sha'abi wani bangare ne na sojojin Iraki, kuma sojojinsa suna bin dokokin soji na yanzu, kuma ya nanata cewa batun keɓe makamai a hannun gwamnati, tana nufin ɓangarorin da ke wajen tsarin hukumomin tsaro ne.
Ma'an ya kara da cewa: Ɓangarorin da ke cikin batun keɓe makamai, ƙungiyoyi ne da ke aiki a waje da tsarin hukumomin tsaro na gwamnati. Yayin da yake nuni ga matsayin shari'a na Hashdush Sha'abi, ya bayyana cewa: Hashdush-Sha'abi wani bangare ne na sojojin Iraki, kuma bisa ga doka mai lamba 40 ta shekara ta 2016, dukkan sojojinsa suna bin dokokin soji na yanzu.
Wata majiya ta tsaro ta Iraki ta kuma ce: An ɗauki shawarar keɓe makamai a hannun gwamnati don nanata wannan batu cewa babu wani jagoranci da ya yi daidai da gwamnati, ko wani jagoranci da ke amfani da makamai a wajen tsarin gwamnati.
Ma'an a ƙarshe ya nanata cewa: Hashdush-Sha'abi wani bangare ne na tsarin tsaro na Iraki.
……….
Ra'ayinka